BBC navigation

Najeriya ta kasa cimma yarjejeniya kan noma

An sabunta: 11 ga Yuli, 2013 - An wallafa a 10:06 GMT
Wani manomin rogo a jihar Osun

Wani manomin rogo a jihar Osun

Najeriya ta gaza cimma ware kashi 10 cikin dari na kasafin kudinta domin zuba wa a bangaren noma, duk da rattaba hannu a kan wata 'yarjejeniya a Moputo, inda ta amince da yin hakan.

Kasar dai na ware kasa da kashi uku cikin 100 na kudaden kasafin kudinta ga bangaren na noma.

Shekaru goma kenan da kasashen Afirka 53 ciki har da Najeriyar, suka sanya hannu a kan yarjeniyar ta Moputo domin habbaka ayyukan noma.

Kasashe bakwai ne da suka hada da Nijar da Mali da Malawi da Senegal da Habasha da Guinea da kuma Burkina Faso suka iya cika wannan alkawari.

A cewar mamba a kwamitin ayyukan noma na majalisar wakilan Najeriya, Muktar Mohammed Ciromawa, laifin rashin aiwatar da yarjejeniyar Moputon na bangaren zartarwa.

Inda ya bayyana cewa a shekarar 2012 an zuba jari a kasar da ya tasanma dalar Amurka biliyan 43, amma ba a sanya ko dala daya ba a bangaren noma.

Sai dai wani mamba a kwamitin, Ahmed Babba Kaita na ganin ita ma majalisar na da rawar da za ta taka na tsayin daka wajen ganin an aiwatar da wannan yarjejeniya na ware kashi 10 cikin dari a kasafin kudin shekarar 2014, domin bangaren noma.

Najeriya dai na samun wasu tallafi na ayyukan noma daga gurare kamar, China da bankin Afrika da na Musulunci, amma har yanzu manoma musamman kanana na yankunan karkara ba sa gani a kasa.

A shekarun baya dai kasar ta dogara ne wajen samun kudin shiga daga ayyukan noma, amma samun man fetur ya sa ta yi watsi da wannan bangaren.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.