BBC navigation

Obama ya jinjina wa demokradiyyar Senegal

An sabunta: 27 ga Yuni, 2013 - An wallafa a 14:31 GMT
Shugaba Obama da mai masaukinsa Macky Sall

Shugaba Obama da mai masaukinsa Macky Sall

Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa kasar Senegal bisa kasancewa daya daga cikin kasashen da dimokradiyyarsu ta girku, tare da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar farko ta ziyarar kasashe uku a Afirka, bayan ganawa da shugaba Senegal Macky Sall, Mr. Obama yace Senegal ta gudanar da zabuka na gaskiya da adalci da kuma mika sauyin ragamar mulki cikin lumana da zaman lafiya.

Cikin batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna sun hada da na tsaro a yankin Afrika ta yamma da kasuwanci.

A lokacin jawabin nasa, shugaba Obama ya bayyana kasashen Saliyo da Liberia da Nijar da kuma Ghana, a matsayin wadanda suma tsarinsu na dimokuradiyyar ya samu gindin zama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.