Batun Syria zai kankane taron G8

  • 17 Yuni 2013
Shugaban Amurka Barrack Obama ya isa Ireland ta Arewa
Shugaban Amurka Barrack Obama ya isa Ireland ta Arewa don hallartar taron G8

Shugabannin Kasashen duniya na hallara a Arewacin Ireland domin gudanar da taron kungiyar G8, inda rikicin Kasar Syria na daga cikin mahimman abubuwan da taron zai duba.

Firai Ministan Birtaniya David Cameron ya ce taron na kwanaki biyu ka iya fito da abubuwa masu kyau, a kokarin da ake yi na kawo karshen rikicin Syria.

Amurka da Rasha ma sun ce suna son a gudanar da tattaunawar samun zaman lafiyar.

To sai dai, yayin da Amurka da wasu kawayenta ke goya wa 'yan tawayen Syria baya, Rasha kuma na goya wa gwamnati baya.

Wakilin BBC ya ce duk wata nasara da aka samu a taron, ka iya zama wani abin da za a yi tutiya a kai.

Mai masaukin baki, Camerona ya nace kan cewa taron na kwana biyu zai lalubo mafita, amma yana fuskantar matukar matsin lamba daga ‘yan majalisa daga bangaren adawa, wadanda ke neman sai lallai a kara tallafa ma ‘yan tawayen Syria.

Shugaba Putin na Rasha dai na da cikakkiyar masaniya cewa da wuya idan kasashen yammacin duniyar za su sauya ra’ayi a kan wannan batu, amma neman mafitar a taron, zai zamo abu mafi muhimmanci.

Karin bayani