BBC navigation

'Yan sanda da masu bore sun sake arangama a Turkiyya

An sabunta: 16 ga Yuni, 2013 - An wallafa a 07:13 GMT
zanga zanga a turkiyya

zanga zanga a turkiyya

Dubban jama'a sun fantsama a kan tituna a birnin Santanbul na Turkiyya, bayan 'yan sanda ta karfin tuwo sun fatattaki masu zanga-zanga daga filin shakatawa na Gezi dake tsakiyar birnin, wanda shi ne birni na biyu mafi muhimmanci a kasar.

Akwai rahotannin dake cewa ana ci gaba da fito-na-fito, sararin samaniyar kuma ya turnuke da hayaki mai sa hawaye, da ya kai nisan kilomita guda daga filin shakatawar.

Hukumomin tsaron kasar dai sun dauki wannan mataki ne bayan da Firayim Minista Recep Tayyib Erdogan ya sake yin kiran da a kawo karshen zanga-zangar.

Abin da ya faro daga zanga-zangar kare muhalli dai, ya rikide zuwa wata gagarumar zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a daukacin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.