BBC navigation

'Yan ta'adda sun kashe soja a London

An sabunta: 22 ga Mayu, 2013 - An wallafa a 20:08 GMT
woolwich

'Yan sanda sun rufe titin zuwa Woolwich dake kudu maso gabashin London

Gwamnatin Birtaniya ta yi zargin cewa, harin ta'addanci ne aka kaiwa wani mutum a nan London, inda aka hallaka shi.

Shaidu suka ce, wasu mutane ne biyu, suka yi ta daba wa mutumen wuka har sai da ya mutu.

Ana jin mutumen soja ne, daga baya 'yan sanda sun harbi maharan, wadanda a yanzu suke can kwance a asibiti.

Praministan Birtaniyar, David Cameron, yayi Allah wadai da abinda ya kira " mummunan kisa".

Mista Cameron ya katse ziyarar da yake yi a Faransa domin komowa gida, inda zai shugabanci taron kwamitin gaggawa na COBRA.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.