Aikin ceto na cigaba a China

  • 21 Aprilu 2013
Wata maata da jaririnta da suka tsira da rayikansu
Mutane sama da dari biyu ne aka tabbatar sun rasu a sakamakon girgizar kasar

Masu aiki ceto a China sun isa bangaran dake da wuyar zuwa a lardin Sichuan na Kudu maso Yammacin kasar, inda girgizar kasa ta afkawa ranar asabar.

Sai dai kuma sai da su ka yi tattaki sosai kafin su isa yankin, saboda kasar da ta zagwanye kan tituna da kuma tafiyar hawainiyar ababan hawan da ake samu a kan tituna suna kawo cikas ga aikin ceton.

Wasu mazauna kauyen Longquan, daya daga cikin kauyukan da bala'in ya shafa, sun ce ba su da ruwan sha da wutar lantarki a kauyen, kuma suna jiran taimakon gwamnatin China da na sauran yankunan kasar.

Bayan ya ziyarci yankin Lushan, watau cibiyar girgizar kasar, Pira ministan kasar ta China , Li Keqiang, ya fada wa manema labarai cewa yanzu abun da suka sa a gaba, shi ne ceto rayukan jamaar da bala'in ya ritsa da su.

An tabbatar da mutuwar sama da mutane dari 2 yayin da wasu dubu 11 suka jikata lokacin da girgizar kasar ta afkawa yankin dake yammacin Chengdu.

Har yanzu dai ba'a san irin ta'arin da girgizar kasar ta yi ba, kuma an tura sojoji da 'yan sanda dubu 17 domin su taimakawa wajan ayyukan ceton.

Yanzu haka dai, an kafa tantuna a wajen babban asibitin birnin Ya'an domin karbar mutanen da suka samu raunika.

Hakazalika a wani mataki na taimakawa masu aikin ceto, hukumomin Chinan sun bada sanarwar dakatar da ba 'yan jarida, izinin ziyartar yankunan da bala'in ya shafa, domin rage cunkoson motoci a kan hanyoyin dake kaiwa yankunan.

Karin bayani