BBC navigation

Amurka ta dakatar da gwajin makamai

An sabunta: 7 ga Aprilu, 2013 - An wallafa a 05:36 GMT

Amurka ta dakatar da gwajin makamai masu linzami

Amurka ta dakatar da wani shiri da ta yi na gwajin makamai masu linzami da ake harbawa tsakanin wata nahiya zuwa wata.

Shawarar ta zo ne a daidai lokacin da ake sa'in sa tsakanin Amurkar da Korea ta Arewa.

An ruwaito wani jami'i a ma'aikatar tsaron Amurkar yana cewa Amurka ta lura cewar duk wani gwaji da za ta yi a yanzu zai kara ruruta rikicin ne.

Mai yiwuwa ne a daga lokacin gwajin zuwa wata mai zuwa.

Cikin 'yan makonnin nan dai hankula sun kara tashi a tsibirin na Korea yayin da rundunar Sojin Korea ta Arewa ta yi kashedin cewa an ba ta umurnin kai hari a kan Amurka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.