BBC navigation

Shugaban Sudan ya ce a saki Fursunonin Siyasa

An sabunta: 1 ga Aprilu, 2013 - An wallafa a 14:59 GMT
Omar Al-Bashir

Shugaban Kasar Sudan

Shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir ya bada umarnin a saki baki dayan firsunonin siyasa na Kasar.

A wani jawabi da yayi a lokacin bude zaman majalisar dokokin kasar, Shugaba Al-Bashir ya kuma yi kira domin a sasinta tare da sauran jam'iyyun siyasa.

A makon jiya ne, mataimakin shugaban kasar Sudan, Ali Osman Taha, ya mika goron gayyata ga 'yan tawaye na Kudancin Kordofan da yankin Blue Nile da su zo a tattauna domin fito da sabon tsarin mulki.

Tuni dai hadin guiwar jam'iyyun adawa da kuma 'yan tawaye na kungiyar Sudan Peoples Libration Movement na yankin Sudan ta Arewa suka yi watsi da kiran da mataimakin shugaban kasar yayi.

Gwamnatin Sudan ta sha yin watsi da batun tataunawa tare da yan tawaye.

Kasar ta Sudan dai in ji masana ta na bukatar sabon tsarin mulki wanda zai maye gurbin daftarin da aka tsara na shekara ta 2005.

A karkashin wannan daftari ne aka tsara yarjejjeniyar sulhun da ta kawo karshen yakin basasa na tsawon shekaru 23 da kasar ta yi fama da shi, wanda ya kai ga kafa kasar Sudan ta Kudu a watan Yuli na shekara 2011.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.