Kotun duniya ta sanya ranar da Kenyatta zai gurfana

  • 7 Maris 2013
Uhuru Kenyatta
Uhuru Kenyatta zai gurfana a Kotun duniya a watan Yuli

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da ke Haque ta sanya ranar 9 ga watan Yuli mai zuwa domin fara shari'ar Uhuru Kenyatta.

Ana tuhumar Mr Kenyatta ne da aikata laifukan cin zarafin bil'adama ta hanyar ingiza fadan da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007 a kasar Kenya.

Da farko a watan Afrilu ne kotun za ta fara sauraran karar amma sai ta dage a watan da ya gabata.

Wakilin BBC a birnin Nairobi ya ce yanzu haka dai ana zaman dar-dar kan tsoron maimaita rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.