BBC navigation

Cardinals za su fara taron zaben Fafaroma

An sabunta: 4 ga Maris, 2013 - An wallafa a 06:21 GMT

Masu mukamin Cardinals a cocin Roman Katolika a yau Litinin za su fara wannan taron sirrin wanda za'a kwashe mako daya ana yi domin zabar sabon Fafaroma bayan murabus din din da Fafaroma Benedict ya yi a ranar alhamis din da ta gabata.

Wanda su ka zaban ne zai jagoranci cocin katolika mai sama da mabiya biliyan daya a duniya.

A mako mai zuma ne ake sa ran za'a fara zaben sabon fafaroma, amma ya zuwa yanzu dai ba a sanya ranar kada kuri'ar ba.

Masu mukamin Cardinals daga fadin duniya dai na ci gaba da isa birnin Rome domin zaben sabon Fafaroma da zai jagoranci cocin Roman Katolika a fadin duniya.

Kashi biyu cikin uku na Cardinals din da ake da su a duniya sun riga sun isa birnin na Rome a karshen makon da ya gabata.

Kasar Burtaniya dai ba za ta samu wakilci ba ba saboda murabus din da Cardinal Keith O'Brien ya yi, bayan ya
amince da zargin yin lallata da ake masa.

Archbishop din Westminster da ya yi murabus wato Cardinal Cormac Murphy O'Connor, zai halarci taron share fage, amma bashi da damar yi zabe saboda ya haura shekaru tamanin.

Amma dai yayi zabe a lokacin da aka zabi Pope Benedict a shekara ta 2005.

A yanzu haka dai za'a tsaurara matakai a Vatican musamman ma game da samun bayanai har sai an zabi sabo fafaroma.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.