BBC navigation

Akalla mutane 40 sun mutu a Pakistan

An sabunta: 3 ga Maris, 2013 - An wallafa a 18:29 GMT
Bom a Karachi

An kai hari kusa da masallacin 'yan Shi'a a Karachi

'Yan sanda sunce wani abu mai karfin gaske ne ya fashe a wani yanki mai cike da jama'a , kusa da masallacin 'yan shi'a.

Wadanda lamarin ya shafa dai maza ne da mata da kuma kananan yara.

Har yanzu kuma 'yan sanda na binciken inda aka binne abubuwan masu fashewa da kuma ko aiki ne na dan- kunar bakin wake.

Shugabannin siyasa da na addini sun yi gaggawar yin allawadai da harin, wanda ya biyo bayan wani tashin hankalin bangaranci da ya taba garin Karachi musamman da kuma wsau sassan Pakistan

Masu tatsauran ra'ayi 'yan sunni sun zafafa hare harensu akan al'ummun tsirarun 'yan shi'a na Pakistan, kuma bama baman da su ka tashi a garin Quetta kadai yai sanadiyyar mutuwar mutane kusan dari biyu tun da aka shiga sabuwar shekara

A watan da ya gabata kotun kolin kasar Pakistan ta yi kira akan hukumomi su bullo da wani tsari na kare musamman 'yan Shi'a idan akai la'akari da karuwar hare haren

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.