BBC navigation

Mutane 80 ne suka mutu a Pakistan

An sabunta: 17 ga Fabrairu, 2013 - An wallafa a 07:11 GMT
Harin da aka kai a Quetta, Pakistan

Bom din da ya tashi a Quetta, Pakistan, ya yi daidai da shagunan da ke kusa

’Yan sanda a Pakistan sun ce yawan mutanen da aka tabbatar sun rasa rayukansu a wani harin da aka kai a birnin Quetta ranar Asabar ya karu zuwa tamanin.

Wannan ne dai hari mafi muni a Quetta tun bayan da wani harin bama-bamai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da casa'in a birnin a farkon wannan shekarar, ya kuma haddasa wata zanga-zanga wadda a karshe ta kai ga kawar da hukumomin yankin.

Kakakin ’yan sandan, Wazir Khan Nasir, ya ce mutane kusan dari biyu ne suka jikkata sakamakon tashin bam din a wata kasuwar kayan gwari wacce ke cike makil da jama’a.

Akasarin wadanda al’amarin ya rutsa da su dai—ciki har da mata da kananan yara—’yan kabilar Hazara ne mabiya mazhabin Shi'a wadanda kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin Sunnah suka sha kai musu hare-hare.

'Me ya sa haka?'

Daya daga cikin wadanda suka shaida faruwar al’amarin, Hussain Ali, ya ce bai ga dalilin da ya sa ake kai musu wadannan hare-hare ba:

“Ina wurin lokacin da abin ya faru, na kuma ruga don kai dauki amma mutanen da suka mutu da wadanda suka jikata suna da yawa matuka. Me ya sa haka ke faruwa ga al’ummar Hazara?”

’Yan sanda sun ce da dama daga cikin wadanda suka jikkata suna cikin wani mummunan yanayi, kuma an debi wadansu daga cikinsu zuwa wadansu asibitoci a birnin Karachi na kudancin kasar.

Wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta mabiya Sunnah, Lashkar-e-Jhangvi, ta ce ita ta kai harin.

Quetta ne dai babban birnin lardin Balochistan na kudancin Pakistan, inda baya ga kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayin addini, kungiyoyin ’yan kishin kasa ke gwagwarmayar neman kari a kudin shigar da kasar ke samu daga iskar gas da albarkatun kasar da ake tatsa a yankin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.