Budurwar Oscar Pistorius za ta fito a Talabijin

  • 16 Fabrairu 2013
Reeva Steenkamp
Gidan talabijin din ya ce zai sadaukar da fitowar shirin ga Reeva Steenkamp

Wani gidan talabijin na kasar Afirka ta Kudu zai yada wani shiri wanda buduwar dan wasan tseren nan na gasar Olympics ta nakasassu wato Oscar Pistorius ta fito a cikinsa.

A cikin Shirin mai suna '”Tropica Island Of Treasure”, budurwar dan wasan Reeva Steenkamp tana gasar ka-cin-ci-ka-cin-ci ne da wadansu mashahuran mutane don samun kyauta.

Oscar Pistorius dai ya musantazargin cewaya kashe ta ne da gangan.

Masu shirya shirin sun ce za a sadaukar da fitowar wannan makon na shirin domin tunawa da marigayiya Reeva.

Karin bayani