Masar ta umarci a haramta shafin YouTube

  • 9 Fabrairu 2013
Tambarin shafin Youtube

Wata kotu a Masar ta yi umarnin sanya haramci na tsawon wata guda akan shafin Internet na Youtube na musayar hotunan vidiyo saboda wasu hotunan ɓatanci ga addinin musulunci da aka sanya a shafin wanda ya haddasa fitina a kasashen musulmi.

Kotun ta birnin Alkahira ta kuma yi umarnin cewa wajibi ne hukumomi su dauki matakai domin toshe dukkan kafar shiga shafin na Youtube.

Kotun ta kuma nemi a toshe wasu shafukan yanar gizo waɗanda suka amince aka sanya bidiyon da aka yiwa lakabi da "innocence of Muslims" wanda ya yi ɓatanci ga manzon Allah.

Wani Lauya ɗan kasar ta Masar Hamed Salem shine ya shigar da ƙarar.