Save the Children ta ce ana yakar talauci

  • 8 Janairu 2013
Save the Children

Kungiyar ba da agaji ta Save the Children ta ce karuwar hadin kai tsakanin kasashen duniya ya haifar da gagarumar nasara a yakin da ake yi da talauci a duniya.

A wani sabon rahoton da ta fitar hukumar ta amince cewa akwai jan aiki a gaba, amma kuma a yanzu za a iya tunanin cewa zai yiwu a magance matsanancin talauci baki daya a fadin duniya a cikin shekaru masu zuwa.

Save the Children ta ce wasu sababbin dabarun za su iya taimakawa wajen tabbatar da cewa babu yaron da ya mutu sandiyar cututtukan da za a iya magance su, kuma kowanne yaro ya je makaranta, sannan kowanne yaro ya samu kariya daga tashe-tashen hankula.