BBC navigation

Sudan da Sudan ta kudu sun cimma matsaya

An sabunta: 7 ga Janairu, 2013 - An wallafa a 10:06 GMT
Mahalarta taron kasashen Sudan da Sudan ta kudu

Mahalarta taron kasashen Sudan da Sudan ta kudu

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta kudu sun amince da aiwatar da matakan da aka tsara na kawo karshen rikicin da kasashen biyu ke fama da shi.

An dai sanar da hakan ne a karshen tattaunawar da shugabannin suka yi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Wakilin kungiyar kawancen kasashen Afrika Thabo Mbeki ya bayyana cewa shugabannin sun tattauna batutuwan da ke da nasaba da yankin Abyei da tsaro da batun aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma da kuma batun kan iyakokin kasashen.

Gabannin tattaunawar dai hukumomin Sudan ta Kudu sun yi zargin cewa Jamhuriyar Sudan ta kaddamar da hare hare a jihar Bahr el-Ghazal dake kudancin kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.