BBC navigation

Ghana za ta samu makamashin rana mafi girma a Afrika

An sabunta: 4 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 13:28 GMT
Gilasai dake tatsar hasken rana

Gilasai dake tatsar hasken rana

Wani kamfanin Birtaniya ya sanar da wani shiri na gina abin da ya kira tashar samar da wutar lantarki ta yin amfani da hasken rana mafi girma a Afrika.

Aikin na Nzema da za a yi a kasar Ghana zai samar da wutar lantarki ga gidaje fiye da dubu 100.

Za a fara aikin gina tashar wutar lantarkin, wanda za a kashewa kimanin dala miliyan 400 a cikin watanni 12 masu zuwa.

Kamfanin da zai gina tashar ya ce, yana da kyakkyawar fata na cewa za a amince da kudaden da za a kashe wajen wannan aikin, a cikin watanni shida.

Girman aikin

Wani kamfani ne mai suna Blue Energy dake Ingila, wanda ke zuba jari a harkokin makamashin da ake sabuntawa, ke yunkurin samar da makamashin na hasken rana a Ghana.

Wannan dai ba shi ne aikin samar da makamashin hasken rana da aka fara sanarwa za a yi a nahiyar Afrika ba, amma babu wanda ya kai shi girma a cewar wani mai sharhi game da al'amuran da suka shafi masana'antu, Ash Sharma na cibiyar bincike na IMS.

Ma'aikata na kafa gilasan dake tatsar hasken rana

Ma'aikata na kafa gilasan dake tatsar hasken rana

Ya ce tashar wutar lantarkin mai karfin megawatt 155 za ta kara yawan wutar lantarkin da Ghana ke samarwa da kashi shida cikin dari.

Mista Sharma ya shaida wa BBC cewa " Aikin shi ne mafi girma da za a yi a halin yanzu. Ba shi ne mafi girma a duniya ba, amma idan an yi, shi zai zamo mafi girma a Afrika."

Ya kara da cewa muhimmin abin da ya kara kaimin aikin shi ne, dokar da Ghana ke da shi game da makamashin da ake sabunta wa, wanda a karkashinta aka bada garanti na kudaden wuta na shekaru 20.

Farashin wutar lantarkin wani garanti ne, na tabbatar da aikin tashar wutar lantarkin ya dore.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.