BBC navigation

Shugaban Masar ya fadada ikonsa

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:04 GMT

Muhammed Morsi, shugaban Masar

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi ya bada sanarwar wani sabon kudurin doka wanda ya fadada karfin ikonsa, a dai dai lokacin da masu zanga zanga suke arangama da 'yan sanda a rana ta hudu a birnin Alkahira.

A wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin, mai magana da yawun shugaban kasar, Yassar Ali ya ce ba wata hukuma da zata sauya shawarwarin shugaban kasar ciki har da bangaran shari'a kuma an yi ne domin kare juyin juya halin kasar ta Masar.

Shugaban kasar ya ce duk mutanen da aka wanke kan kisan masu zanga zanga a lokacin juyin juya halin za'a sake yi musu shari'a.

Bayanin na shugaba Morsi ya zo a dai dai lokacin da masu zanga zanga su kai arangama da 'yan sanda a rana ta hudu ta zanga zangar da suke a birnin Alkahira.

An yi arangarmar ne a kusa da dandalin Tahrir, inda mutane da dama suka rasa rayukansu a fito na fiiton da aka yi tsakanin shugabannin sojin kasar da masu zanga zanga a watan Nuwambar bara.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.