BBC navigation

'Yan bindiga sun kashe mutane biyar a Bani Walid na Libya

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 04:43 GMT

'Yan Libya dauke da bindigogi

Wasu 'yan bingida sun yi ta luguden wuta a garin Bani Walid na kasar Libya, inda suka kashe akalla mutane biyar tare da raunata wasu da dama.

Rahotanni sun ce maharan tsofaffin 'yan tawaye ne da yanzu ke da alaka da sojojin Libya.

Majalisar dokokin Libyan dai ta bada umurnin yin amfani da karfi don gano wadanda suka kashe Omar Sha'aban, mutumin da aka danganta shi da cafke marigayi kanar Gaddafi a bara.

Bani Walid dai gari ne da yake da magoya bayan marigayi kanar Ghaddafi tsawon lokacin da aka yi masa bore a kasar har lokacin da aka hambarar da shi aka kuma kashe shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.