
Shugaban Sudan da na Sudan ta Kudu
A ranar Litinin ne shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su ci gaba da tattaunawa game da rashin jituwar da ta kusa kai su yaki a farkon shekarar nan.
Muhimman batutuwan da tattaunawar ta keke-da-keke za ta maida hankali sun hada da sha'anin tsaron bakin iyakokin kasashen.
Yadda za a raba kudaden da ake samu ta hanyar fitar da man fetur da kuma yankin Abyei da ake takaddama akai.
Shugabannin biyu dai na tattaunawar ce a Habasha.
An dage tattaunawar ce ranar Lahadi bayan shugabannin sun kwashe fiye da sa'oi biyu suna yin ta.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar sanyawa kasashen biyu takunkumi, idan ba su cimma wata kwakkwarar yarjejeniya ba.













