
Alkalin wasa Mark Halsey a filin wasa
Alkalin wasan da ya yi alkalancin wasan Liverpool da Manchester United Mark Halsey, ya kai kuka ofishin 'yan sanda bayan da ya sha zagi ta shafin twitter bayan wasan.
A wasan dai da Manchester United ta ci Liverpool biyu da daya an bawa Jonjo Shelvey jan kati a farkon wasan inda suka gama wasan da 'yan wasa goma.
Bayan an tashi daga wasan dai an ta turawa Alkalin wasan Mark Halsey sakon cin mutunci ta shafin twitter.
Halsey ya shaidawa BBC cewa iyalan sa sun kai kara ofishin 'yan sanda.












