
Jirgin sama
Gwamnatin Ivory Coast ta ce za ta sake bude sararin samaniyarta ga kasar Ghana don bai wa jiragen kasar damar sauka.
Sai dai hukumomi sun ce Ivory Coast za ta ci gaba da rufe iyakokin ruwa da na kasanta da Ghana.
Ofishin shugaba Allassane Ouattara ne ya bayar da sanarwar ta talabijin na kasar.
Kasar ta Ivory Coast ta rufe iyakokin ta da Ghana ne a ranar Juma'a sakamakon wasu hare-hare da aka kai wa jami'an ta a wasu wuraren binciken ababen hawa inda aka kashe mutane da dama.
Jami'an kasar ta Ivory Coast sun dora laifin wadannan hare-hare a kan magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo da ke gudanar da harkokin su daga Ghana.












