
Wang Lijun
Wata Kotu da ke birnin Chengdu ta yanke wa tsohon babban jami'in 'yan sandan China hukuncin daurin shekaru goma sha biyar a gidan yari saboda hannun da yake da shi a wata tabargazar siyasa.
An tuhumi Wang Lijun ne da laifukan da suka hada da sauya sheka, da amfani da matsayinsa ba bisa ka'ida ba, da kuma neman yin rufa-rufa ga kisan wani dan kasuwa dan Birtaniya.
Ya amsa laifukan da aka tuhume shi da aikatawa.
A cikin watan Fabrairu ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Amurka, ya kuma yi zargin cewa Gu Kailai, uwargidan fitaccen dan siyasar nan na China, Bo Xilai ta kashe abokin huldar cinikin ta ne a rikicin da suka yi game da kudi.


















