
Libya na fama da haramtattun kungiyoyi dauke da makamai
Dakarun kasar libya sun baiwa kungiyoyin dake dauke da makamai a cikin Kasar wa'adin sa'oi 48, dasu fice daga cikin gine- ginen gwamnati
Jami'ai sunce tuni aka fatattaki wata haramtacciyar kungiya daga sansaninta akan babban titin dake danganawa zuwa filin jirgin Kasar na kasa da kasa, kusa da babban birnin Kasar na Tripoli
Wa'adin dai, ya biyo bayan kisan jakadan Amurka a birnin Bengazi a wannan watan
A ranar asabar dai aka fatattaki kungiyar nan da ake zargi da kisan jakadan Amurkan daga sansaninta a Bengazi, bayan wata gagrumar zanga zanga













