BBC navigation

Shugabannin Sudan za su yi taro

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:10 GMT

el-Bashir da Salva Kiir

Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu za su gana a kasar Ethiopia a wani muhimmin taron koli da zai tattauna batun tsaron iyaka da hakar man fetur.

Masu shawarwarin sasantawa a bangarorin biyu sun ce an samu muhimmin ci gaba kafin ganawar da shugabannin za su yi.

Sudan ta Kudu, wadda ta samu 'yancin kai a bara, ta dogara ne da hanyoyin tura mai na Sudan wajen tallan manta ga kasashen duniya.

Ta dakatar da hakar mai ne bayan Sudan ta fara dibar man a madadin kudin haraji na hanya.

An cimma yarjejeniya tsakanin kasashen a watan Agusta amma kasar Sudan ta nace kan sai an warware matsalolin tsaro kafin Sudan ta Kudu ta koma aikin tura man fetur ta bututun da ya ratsa kasar ta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.