
Masu zanga-zanga sun kona wani ginin sojin sa-kai a Benghazi
A birnin Benghazi na kasar Libya, dubban talakawa masu bore da sojoji sun yi arangama da 'yan kungiyoyin sojin sa-kai, inda suka farma sansanonin 'yan kungiyoyin sa-kan.
Sun kutsa kai cikin sansanonin inda aka kashe akalla mutane hudu tare da raunata kimanin arba'in.
Masu zanga-zangar sun nuna rashin amincewa da karfin ikon da kungiyoyin sa-kan suke da shi, suna masu cewa tun bayan kawar da tsohon shugaban kasar, Kanar Mo'ammar Gaddafi ne kungiyoyin sa-kan ke rike da miyagun makamai.
A cewarsu, kungiyoyin suna musgunawa jama'a da kuma yin barazana ga tsaron kasar.
Sun yi kira ga hukumomi da su kwace makamai daga hannayen 'yan kungiyoyin sa-kan, kana su tabbatar da doka da oda.
Lamarin ya fi muni a sansanin kungiyar sojin sa-kai ta Ansar Al-shari'a, wacce ake zargi da kai harin makon jiya, lokacin da aka kashe jakadan Amurka, Chris Stevens.













