
Ms Ngozi Okonjo-Iweala, Ministar Kudi ta Najeriya
Gwamnonin jihohi 36 a Najeriya sun bayyana cewa za su sake garzayawa zuwa kotun kolin kasar don ci gaba da shari'a da gwamnatin tarraya game da maganar ajiyar kudin rarar mai a asusun ajiyar kudin don amfani da su a gaba, wato Sovereign Wealth Fund a turance.
Gwamnonin na so ne a ci gaba da bin tsarin da ake bi a halin yanzu wajen rabon kudin rarar man.
A tsarin na yanzu dai ana tara kudade ne a asusun rarar kudaden man fetur, wanda ake rabawa daga lokaci-zuwa lokaci, kowacce jiha ta kwashi dauninta da zarar kudin sun taru, wato Excess Crude Account a turance.
Sai dai Ministar Kudi ta Najeriya, Ngozi Okonjo - Iweala ta ce da yardar Gwamnonin aka kafa wannan asusu.


















