
Ana kwaso 'Yan gudun hijirar Habasha dake Yemen
Ana kwaso 'yan gudun Hijira 'yar kasar Habasha dake Yemen zuwa babban birnin kasar Habashan na Addis Ababa.
Kungiyar da ke kula da masu gudun hijira ta kasa da kasa ta ce an kwaso 'yan gudun hijira 'yan kasar Habashan fiye da 500 a wannan makon, yayinda ake saran kwaso wasu 300 a mako mai zuwa.
Kungiyar tace 'yan gudun hijirar na daga cikin 'yar kasar Habasha dubu hudu dake zaune a budadden waje a arewa maso yammacin Yemen, wanda su ka kasa samun damar shiga cikin kasar Saudi Arabiya inda suke fatan samun aikin yi












