
An jefa bam a wani gidan mai a Syria
Kungiyoyin 'yan adawa a Syria sunce an kashe akalla mutane talatin, lokacin da wani jirgin soji ya jefa bam a wani gidan man fetur dake arewacin kasar.
Ance an jiwa mutane da dama raunuka a harin.
Gidan man dai na kusa da garin Ain Issa, mai tazarar kilomita 30 daga kan iyakar shiga kasar Turkiyya.
Mayaka 'yan tawaye dai sun kwace garin Ain Issan ne a ranar Laraba.
Masu fafutuka sunce akwai gungun mutane da yawa su na jiran mai a lokacin da aka jefa bam din.













