
An kai harin kunar bakin wake a birnin Mogadishu
Wasu 'yan kunar-bakin-wake biyu sun tayar da bama-bamai a wani gidan abinci dake babban birnin Somalia, Mogadishu, inda su ka kashe kansu da akalla mutane 14.
Wurin abincin na kusa da gidan nuna wasan kwaikwayo na kasar ne, inda 'yan jarida da 'yan siyasa ke yawan halarta.
Tsohon editan gidan talabijin na Somaliyan da wasu 'yan jarida biyu da 'yan sanda biyu na daga cikin wadanda aka kashe.
Wani ganau yace ''an kai harin ne a wurin da yawanci 'yan jarida da 'yan Somaliya da su kaje kasashen waje ke taruwa su na tattaunawa, su na shan kofi, su na kuma samun labarai."
Dakarun tsaro sun yiwa wurin kawanya.













