
Barnar da wani harin ya yi a Mogadishu
Wasu 'yan kunar-bakin-wake biyu sun tayar da bama-bamai a wani gidan abinci da ke Mogadishu, babban birnin Somalia inda suka kashe kansu da akalla mutane goma sha hudu.
Gidan abincin wanda ke dab da gidan nuna wasan kwaikwayo na kasar wuri ne da 'yan jarida da 'yan siyasa ke yawan halarta.
Tsohon editan gidan talabijin na Somalia, da wasu 'yan jarida biyu da 'yan sanda biyu suna daga cikin mutanen da aka kashe.
Wani dan jarida mai daukar hoto a wajen ya bayyana yadda bama-baman suka yi kaca-kaca da kawunan 'yan kunar bakin-waken, yana mai cewa jinin mutane ya fantsama ko'ina a gidan abincin.
Shugaban kasar ta Somalia, Hassan Sheikh Mahmud, ya yi Alla-wadai da harin.













