
Obama da Clinton
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kashe dala 70000 a kan tallace-tallacen da ta bayar a gidajen talabijin na kasar Pakistan da zummar rage kaifin bacin ran da wani fim da aka yi a kasar, wadanda ya yi batanci ga addinin musulunci, ya jawo.
Tallace-tallacen sun nuna shugaba Obama da Sakatariyar wajen Amurka, Hillary Clinton na yin Alla-wadai da fim din.
Mista Obama ya bayyana Amurka da cewa kasa ce da ke mutunta kowane addini don haka ba ta da muradin cin zarafin kowane addini.
Ita ma Sakatariya Clinton ta ce gwamnatin Amurka ba ta da hannu a shirya fim din wanda aka yi a jihar Califonia.
Dubban jama'a ne suka yi yunkurin yin gagarumin maci zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke Islamabad ranar Alhamis, sai dai 'yan sanda sun hana su.
Gwamnatin Pakistan ta bai wa 'yan kasar hutu ranar Juma'a domin su samu damar gudanar da gangamin nuna kyama ga fim din.


















