
Laurent Fabius, Ministan harkokin wajen Faransa,
Faransa ta ce za ta rufe wasu ofisoshin jakadanci da makarantu a kasashe ashirin ranar Juma'a, bayan da wata mujallar Faransa ta wallafa wasu zane-zane na batanci ga Annabi, Sallahu Alaihi wasallam.
Hakan ya biyo bayan fargabar cewa lamarin na iya kara tayar da kurar rikici bayan sallar Juma'a.
Kasar ta ce rufe ofisoshin na wani dan lokaci ne bayan sallar juma'a.
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce ya damu da hotuna ashirin da aka buga, a mujallar ta Charlie Hebdo, mai yin shagube.
Ya ce, "Na bada umurni a dauki matakan tsaro na musamman a dukkan kasashen, inda za a iya fuskantar barazana, kuma Fransawa su kasance masu taka tsantsan."
Ko a watan Nuwambar bara an kai harin bam a kan ofishin mujallar bayan wallafa irin wadannan hotunan na batanci ga Manzon Allah, SAW.


















