
Shugaban sashen ayyukan kiyaye zaman lafiya na
Shugaban sashen ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Herve Ladsous ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa 'yan tawaye sun kafa abin da ya kira, wata gwamnatin wucingadi a gabashin jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Mr Ladsous ya ce 'yan tawayen na kungiyar M23 na iko da mazauna yankin, suna kuma karbar haraji.
Majalisar Dinkin Duniya dai na zargin Rwanda da mara baya ga 'yan tawayen na kungiyar M23.
A halin da ake ciki, hukumomin jamhuriyar Congon na neman an haramtawa Rwanda dillancin ma'adinan da aka haka a Congon.
Ministan ma'adinai na Congo ya rubuta wasika ga Amurka da Birtaniya yana kira ga kampanoninsu da su daina sayen ma'adinai daga Rwanda, wadanda galibi daga kasar Congo ake hakowa.













