BBC navigation

Arik Air ya dakatar da zirga-zirga a Najeriya

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:09 GMT
Arik Air

Arik Air shi ne kamfanin jiragen sama mafi girma a Najeriya


Kamfanin jiragen sama na Arik Air a Najeriya ya dakatar da zirga-zirgar a dukkan fadin kasar, bayan da ya zargi hukumomi da muzguna masa.

Shugaban kamfanin Chris Ndulue, ya ce ministar kula da harkokin jiragen sama ta kasar da wasu mutane na kokarin kashe harkar saboda cimma wasu bukatunsu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya rawaito.

Kamfanin Arik ya kuma ce jami'an ma'aikatar kula da zirga-zirgar jiragen sama sun kai sumame a ofishinsa da ke Legas, inda suka kawo tsaiko ga zirga-zirgar jirage.

Sai dai wata sanarwa daga ma'aikatar kula da zirga-zirgar jiragen saman ta musanta cewa jami'anta sun kai sumame ofishin Arik, suna masu dora alhakin hakan kan kungiyoyin kwadago.

Sanarwar ta kara da cewa ma'aikatar bata da hannu a matsalolin da Arik ke fuskanta.

Matakin na Arik Air zai kara munana halin da ake ciki a fannin zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya.

Har yanzu kasar bata gama farfadowa daga hadarin jirgin saman da ya kashe fiye da mutane 160 a watan Yunin da ya gabata ba.

Tuni dai jama'a a kasar suka fara nuna damuwa kan labarin da kuma hasashen irin illar da zai haifar ga harkokin zirga-zirga da kuma kasuwanci a kasar.

A sakon da ya wallafa a shafin Twitter na BBC Hausa, M S Alkali ya ce "amma sun kusa ritsawa da mu domin sati mai zuwa muke niyyar sayen tikitinsu, Allah ya tsare".

Wannan matakin na Arik Air ya shafi dukkan zirga-zirga 100 da kamfanin ke yi a fadin Najeriya - shi ne dai kamfanin jiragen sama mafi girma a kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.