
Ana ci gaba da fafatawa a Syria
A yau ne hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ke mahawara akan batutuwan da su ka shafi keta hakkin bil'adama a kasar Syria.
Hukumar na tattaunawa ne a kan wani rahoto da aka buga a karon farko a watan agusta, wanda ya zargi dukkanin bangarorin gwamnati da 'yan tawayen kasar da aikata laifukan yaki.
Shugaban ayarin binciken Paulo Pinheiro ya ce su na da kwakkwarar hujja a kan hakan
Paulo Pinheiro ya kara da cewa su na da sunayen wadanda ake zargi da aikata laifukan yaki.
Ita ma Jukliette De Rivero, ta kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights watch, cewa ta yi ya kamata kotun binciken laifukan yaki ta ICC ta cikin shigo lamarin:

















