
Burma ta saki fursunoni
Kasar Burma ta sallami fiye da fursunoni 500, kuma ana sa ran da yawa daga cikin 'yan siyasar kasar da ake rike da su na cikin wadanda aka sallama.
Jam'iyyun adawa sun ce har yanzu ana tsare da fursunonin siyasa dari hudu duk kuwa da cewar gwamnatin farar hular da ta gabata ta musu afuwa.
An dauki matakin sakin fursunonin ne mako guda kafin ziyarar da shugaban kasar Then Sein ya kai Majalisar Dinkin duniya a birnin New York na Amurka .
Shugaban dai na neman goyon bayan kasashen duniya game da sauye sauyen da ya ke yi.













