
Hamid Karzai, shugaban Afghanistan
Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai yayi matukar Allah wadai da kisan da aka yi ma wasu mata takwas, a wani hari da NATO ta kai ta sama.
Sanarwa da shugaba Hamid Karzai ya fitar akan kisan matan takwas dai na cike da kalmomi masu nauyin gaske na yin Allah wadai.
Shugaba Karzai ya kuma ce zai aike da jami'ai zuwa lardin da lamarin ya faru domin a soma binciken tabbatar da hakikanin abinda ya auku.
Jami'an lardin Laghman sun ce wasu mata ne na yankin suka fita sassafe zuwa kan wasu tsaunuka domin kalato itacen girki. Kwatsam sai hari daga sama yayi ajalinsu.
Sai dai kuma kakakin dakarun kasashen waje da NATO ke jagoranta yace, hakika sun kai hari da ya nufi masu tada kayar baya, kuma an kashe da dama daga cikinsu.
Amma kakakin na dakarun NATO ya kuma ce, hakika suna sa ne da cewa, harin ya shafi fararen hula, kuma ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Batun kai hari dake shafar fararen hula A Afghanistan yana da sarkakiya sosai a Afghanistan, kuma batu ne dake ingiza kyamar dakarun kasashen waje dake kasar.
Wannan hari na faruwa ne kuma bayan 'yan sandan Afghanistan sun bada rahoton cewa, wani jami'in tsaron kasar ya kashe dakarun NATO hudu.


















