
Jirgin ruwan yakin Amurka a kan teku
Jiragen ruwan yaki kimanin talatin ne suka taru a gabar tekun kasar Bahrain, domin gano tare da kawar da nakiyoyin da aka dasa a cikin ruwa.
Kasar Amurka ce ke jagorantar jiragen ruwan yakin daga kasashen duniya 30.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake cikin wani yanayi na damuwa a yankin game da shirin nukiliyar kasar Iran.
Rundunar mayakan ruwan ta Amurkar ta bayyana atisayen na cire nakiyoyin, a matsayin mafi girma da aka taba gudanar wa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Inda ta ce jiragen za su yi gwajin ne ta yadda za su iya tunkarar duk wani harin nakiyoyi, tare da share hanyoyin dake cikin tekun.
Mahukuntan kasar Iran dai sun jaddada cewa shirin nukiliyar na lumana ne, amma kasashen yammacin duniya na kallon sa da wata siga ne, inda suke zargin cewa kasar na yunkurin kera makaman nukiliyar ne.













