
Masu zanga-zangar nuna kin jinin kasar Japan a China
Kamfanin kera lataronin nan na kasar Japan, Panasonic ya dakatar da wasu ayyukansa na wucin gadi a kasar China, bayan masu zanga-zangar nuna kin jinin Japan sun kai hari kan biyu daga cikin masana'antun Panasonic.
Kamfanin ya ce, masana'antarsa da ke Qingdao za ta cigaba da kasancewa a rufe, har ya zuwa 18 ga watan Satumba.
Kamar yadda wasu rahotanni suka nuna, kamfani Canon shima ya dakatar da ayyukansa a uku daga cikin masana'antunsa.
Haka kuma zanga-zangar da ta bazu a fadin kasar China, ta kuma shafi sauran kamfanoni kamar na Toyota.
Zanga-zangar dai ta fara ne bayan kasar Japan ta ce ta amince da yarjejeniyar sayen tsibiran nan dake gabashin kasar China, da ake takaddama a kansu daga wadanda ta ce sun mallaki tsibiran.
China dai ta ce ita ke da ikon mallakar tsibiran, wadanda har ila yau Taiwan ta yi ikirarin mallaka.













