
Wani sojan Burtaniya a Lardin Helmand na Afghanistan
Wani mutum sanye da kayan 'yan sandan Afghanistan ya bindige sojojin Burtaniya 2 har lahira a wani wurin bincike da aka kafa a Kudancin kasar ta Afghanistan.
Sai dai an kashe wanda ya kai harin a musayar wutar da aka yi wadda ta zo kwana daya bayan mayakan Taliban su kashe wasu Sojan Amurka 2 a lardin Helmand.
A bana dai an samu karuwar hare-haren da jami'an tsaron kasar ke kaiwa dakarun kasashen waje.
Tun farkon wannan watan, jami'an Amurka a Kabul sun sanarda wani shiri na bincike mai tsauri cikin rundunar 'yan sandan kasar ta Afghanistan, sun kuma dakatar da horarda wasu sabbin kurata.













