
Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta
Amurka za ta tura wata tawagar sojojin ta zuwa Sudan bayan hare-haren da aka kai a kan ofishin jakadancin ta dake can.
Harin dai wani bangare ne na boren da ake yi akasari mai muni, a kusan kasashen Musulmi ashirin ga Amurkar da Kawayen ta; bayan fitarda wani fim da aka yi a Amurka wanda ya harzuka musulmi.
Mutane a kalla bakwai aka ce an kashe a Sudan da Tunis da Alkahira ranar jumu'a a cikin tarzomar.
Masu boren a Khartoum babban birnin Sudan sun farfasa taagogi da cinna wuta a ofishin jakadancin Jamus, inda suka kekketa tutar ta suka maye gurbin ta da wata tutar ta Musulunci:-













