
Christopher Stevens Jakadan Amurka wanda aka kashe a Libya
Shugaba Barack Obama na Amurka ya halarci wani buki da aka yi na karbar gawarwakin Jakadan Amurkar a Libya da wasu Amurkawan ukku da aka kashe a harin da aka kai ofishin jakadancin kasar.
A yayinda aka isa da akwatunan gawarwakin a wani sansanin mayakan sama dake kusa da Washington, Mr Obama ya ce ba za a taba mantawa da sadaukar da kanda suka yi ba.
Ya yi alkawarin kamo wa da gurfanarda wadanda suka haddasa mutuwar ta su a Benghazi a ranar talata.
Mr Obaman yace duk da adawar da take fuskanta a wasu kasashe, Amurka ba ta za gajiya ba "wannan shine sakon da kowannenmu ke aikewa a kodayaushe, farar hula ne ko soja ga mutanen dake wani sako na duniya cewa Amurka kawa ce, kuma ba wai bukatun mu kawai muka daamu da su ba, har da na su bukatun.''












