
Yahya Jameh, shugaban Gambia
Shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh ya jingine aiwatar da hukuncin kisa a kan wasu fursunoni da aka yanke ma wannan hukunci.
Fadar shugaban kasar ta ce an dauki matakin hakan ne sakamakon dimbin kiraye kiraye na afuwa.
Kasashen duniya sun yi ta sukar lamirin shugaban kasar ta Gambia a watan jiya, lokacin da ya bada sanarwar dawo da aiwatar da hukuncin kisa.
Daga baya an kashe wasu fursunoni tara ta hanyar harbewa.
A da, shugaban kasar ya ce zuwa tsakiyar wannan wata na Satumba, za a aiwatar da hukuncin kisa a kan daukacin fursunoni arba'in da bakwai da aka yanke ma irin wannan hukunci.













