
Hisam Qandil, Praministan Masar
Masar ta yi kira ga Amurka da ta dauki matakan ganin ba a sake aikata irin abubuwan cin fuska da videon da aka sa a intanet ya yi wa addinin Musulunci ba.
Lamarin dai ya haddasa zanga zanga a kasashen Larabawa, da ma sauran wasu kasashe.
Praministan kasar ta Masar, Hisham Qandil ya shaidawa BBC cewa an ci fuskar mutane kimanin biliyan daya da rabi.
Hisham Qandil ya ce, ba za a lamunci cin fuska ga annabinmu tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi ba.
A Amurka, 'yan sanda sun yi tambayoyi ga daya daga cikin wadanda ake zargi suna da hannu wajen shirya fim din.
Jami'an shari'a na gudanar da bincike domin gano ko ya karya ka'idojin daurin da aka yi masa na baya.













