
Wani hari da aka kai a Afghanistan
Rundunar dakarun kasashen duniya a Afghanistan ta amsa cewar mayakn Taliban sun samu sukunin kai hari a kan daya daga ciki muhimman sansanoninta ne, bayan da suka gano rauni a matakan tsaron da ake dauka.
Ta ce mayakn sun gano wani wuri ne maras tsaro a sansanin na Bastion dake lardin Helmand, suka shiga ciki ta wurin, suka kai hari a filin jirgin saman.
Birgediya Janar Gunter Katz shi ne kakakin runduna kuma yace: " 'yan bindigar sun yi harbi da kananan bindigogi a kan filin jirgin. Alokacin fadan , mun yi asarar dakarun Amurka biyuan kuma kashe 'yan bindiga goma sha takwas.
Taliban ta ce ta kai hari a sansanin ne, ta wani bangaren, saboda Yarima Harry, na uku a jiran gadion sarautar Birtaniya, yana can, a matsayin matukin helikwafta.













