
Mayakan Taliban
Wani hari da mayakan Taliban suka kai kan wani babban sansanin sojojin kasashen waje a Afghanistan ya halaka akala sojan Amurka biyu.
Hakama wasu karin Amurkawan biyar sun samu raunukka a cikin harinda aka kai kan sansanin Camp Bastion dake lardin Helman.
Yarima Harry, Kyaftin a Sojan Burtaniya na a cikin sansanin lokacinda aka kai harin amma bai samu rauni ba.
Rundunar Sojan Amurkar dai ta tabbatarda mutuwar sojan biyu a harin yayinda wasu rahotannin dake fitowa daga Afganistan din suka ce mayakan taliban 16 sun mutu a cikin harin.
Sanarwar ta Taliban
Kungiyar ta Taliban fitar da wata sanarwa inda tace ta kai harin ne a zama ramuwar gayya kan fitarda film din ke muzanta addinin musulunci da Amurkawa suka yi.
Sanarwar wadda ta fito daga wani mai magana da yawun kungiyar Yusuf Ahmadi Qari, wadda bbc ta samu, tace mujahidai masu neman shahada gommai ne suka afkawa sansanin wadanda ta kira 'abokan gaba' na biyu mafi girma a kasar da ta kira 'daular Islama'.
Tace haka kuma mujahidan sun samu kashe wadanda ta kira 'sojan mamaya' gommai kuma suka lalata jiragen saman yaki da masu saukar ungulu samfuri Apache da Chinok masu yawa.
Sanarwar tayi da'awar cewar sansanin na can na ci da wuta kuma bakin hayaki ya turnuke shi yayinda harin ke cigaba.
Ta kara da cewar Kungiyar ta tsara kai wasu hare-haren a wasu sassan kasar a wani bangare na ramuwa ga cin zarafin da aka yiwa Annabi Muhammadu Alaihissalatu wassalam.













