
Masu zanga-zanga a Alkahira
Zanga-zangar nuna kyamar wani fim da aka yi a Amurka wanda ya muzanta Musulunci ta yadu zuwa kasashen Musulmi da dama.
A Tunisia, masu zanga-zanga sun kutsa kai cikin harabar ofishin jakadancin Amurka, inda suka kunna wata wuta ganga-ganga.
Gidan talabijin na Tunisia ya ce an kashe mutane uku a wata hatsaniya tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro.
A Khartoum, babban birnin Sudan kuma, masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin ofishin jakadancin Jamus, inda suka kekketa tutar kasar ta Jamus suka maye gurbinta da wani kyalle mai dauke da rubutun Musulunci.
An kuma kai hari a kan karamin ofishin jakadancin Birtaniya, yayinda masu zanga-zangar gungu-gungu suka shiga harabar ofishin jakadancin Amurka.
Zanga-zangar ta kuma yadu zuwa Najeriya, da India, da Malaysia, da Indonesia, da Birtaniya.


















