
Gwamnatin India ta ki janye karin farashin mai
Majalisar zartarwa ta India ta yanke shawarar kyale manyan shagunan sayar da kayayyaki su bude rassa a kasar, inda a kan samu biliyoyin daloli a harkar saye da sayar da kaya dai-dai.
Ga alama kuma wannan wani yunkuri ne na yin kaimi ga tattalin arzikin kasar wanda ke tangal-tangal.
Wannan mataki dai zai bayar da dama ga manyan shagunan sayar da kayayyaki irin su Wal-Mart da Tesco su hada gwiwa da kamfanoni na gida don rika sayar da kaya kai-tsaye ga mabukata a India.
An fara gabatar da wannan shawara ce shekara guda da ta wuce, amma gwamnatin kasar a karkashin jagorancin jam'iyyar Congress ta sauya tunani bayan jam'iyyun da ke hadaka sun nuna adawa.
Sanarwar dai ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen da ake yi mata ta sauya shawara dangane da karin kudin man fetur da ta yi kwanan nan.


















