
Yara manyan gobe
Yawan yaran dake mutuwa kafin su cika shekaru biyar a duniya sun yi matukar raguwa a shekaru 20 da suka gabata, a cewar asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF.
Kimanin yara 'yan kasa da shekaru biyar, sama da miliyan shida ne suka mutu a shekarar 2011, idan aka kwatanta da mutuwar yara miliyan 12 a shekarar 1990.
Kuma kusan yara 'yan kasa da shekaru biyar dubu 19 ne, suka mutu kullum a shekarar ta 2011.
Asusun na UNICEF ya ce kasashe matalauta na samun kudi, shi yasa aka samu raguwar mace-macen yaran.
Yayin da samun karbuwar shayar da yara nonon uwa da kuma alluran rigakafin cututtuka suma sun taimaka wajen raguwar da aka samu.
Haka kuma matukar raguwar mace-macen yaran an fi samunsa a kasashen da suka samu tallafi daga waje.
Daraktan UNICEF a Birtaniya, David Bull ya ce " Idan ka kalli kasashen da suka samu nasara kamar jamhuriyar demokradiyyar Lao da Timor da kuma Liberia su ne kasashe uku na gaba-gaba, kuma samun agaji ya taimaka matuka."
Yunkurin rage cututtuka masu yaduwa kamar bakon dauro, ya rage mace-macen dake da dangantaka da hakan a fadin duniya.
Alkaluman sun ragu daga dubu 500 a shekarar 2000 zuwa dubu dari a shekarar 2011.













